Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ammonites: Jews intermarry with

35 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Jews intermarry with

  1. Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila.

  2. Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”

  3. Mutanen kuwa suka tā da murya da ƙarfi suka ce, “Gaskiya ka faɗa, dole mu yi yadda ka ce,

  4. Amma akwai mutane da yawa, kuma lokacin damina ne; saboda haka ba za mu iya tsayawa a waje ba. Ban da haka ma, aikin nan ba na kwana ɗaya ko biyu ba ne, domin ba ƙaramin laifi muka yi ba.

  5. Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.”

  6. Yonatan ɗan Asahel, da Yazehiya ɗan Tikba su ne kaɗai ba su yarda da wannan shirin ba, sai Meshullam da Shabbetai Balawe kuma suka goyi bayansu.

  7. Sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi yadda aka zartar. Ezra firist ya zaɓi mutane waɗanda su ne shugabannin iyalai, ɗaya daga kowane sashe, aka rubuta sunan kowannensu. A ranar ɗaya ga watan goma kuwa suka zauna don su yi binciken waɗannan abubuwa.

  8. A rana ta farko ga watan farko, suka gama da bincike duk waɗanda suka auri baƙin mata.

  9. A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya.

  10. (Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.)

  11. Daga zuriyar Immer, akwai Hanani da Zebadiya.

  12. Daga zuriyar Harim, akwai Ma’asehiya, Iliya, Shemahiya, Yehiyel da Uzziya.

  13. Daga zuriyar Fashhur, akwai Eliyohenai, Ma’asehiya, Ishmayel, Netanel, Yozabad da Eleyasa.

  14. Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.

  15. Daga mawaƙa, akwai Eliyashib. Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai Shallum, Telem da Uri.

  16. Ga sunayen sauran mutanen Isra’ilan da suke da wannan laifi. Daga zuriyar Farosh, akwai Ramiya, da Izziya, Malkiya, Miyamin, Eleyazar, Malkiya da Benahiya.

  17. Daga zuriyar Elam, akwai Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot, da Iliya.

  18. Daga iyalin Zattu, akwai Eliyohenai, Eliyashib, Mattaniya Yeremot da Zabad da Aziza.

  19. Daga zuriyar Bebai, akwai Yehohanan, Hananiya, Zabbai, da Atlai.

  20. Daga zuriyar Bani, akwai Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot.

  21. Daga zuriyar Fahat-Mowab, akwai Adna, Kelal, Benahiya, Ma’asehiya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi, da Manasse.

  22. Daga zuriyar Harim, akwai Eliyezer, Isshiya, Malkiya, Shemahiya, Simeyon,

  23. Benyamin, Malluk da Shemariya.

  24. Daga zuriyar Hashum, akwai Mattenai, da Mattatta, Zabad, Elifelet, Irmai, Manasse, da Shimeyi.

  25. Daga zuriyar Bani, akwai Ma’adai, Amram, Yuwel,