Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ammonites

135 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar.

  2. Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai;

  3. zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  4. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.

  5. Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.

  6. Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji.

  7. “Na ji irin zagin da Mowab take yi, da kuma ba’ar Ammonawa, waɗanda suka zagi mutanena suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu.

  8. Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”

  9. Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu, saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki.

  10. Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar. Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada, kowa a ƙasarsa.