Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions Made Beneficial

104 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.

  2. “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.

  3. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’

  4. Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,

  5. yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.

  6. Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Sela

  7. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

  8. yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

  9. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.

  10. Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana.

  11. Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

  12. Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.

  13. A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.

  14. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.

  15. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.

  16. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.

  17. Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka.

  18. Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara.

  19. Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki.

  20. Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.”

  21. A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  22. Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub za su komo ga Maɗaukaki Allah.

  23. Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.

  24. Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala.

  25. Kai kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji.