Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions Made Beneficial: In leading us to seek God in prayer

8 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da In leading us to seek God in prayer

  1. Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.

  2. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna.

  3. Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.

  4. Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.

  5. Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi.

  6. Gama zan zama kamar zaki ga Efraim, kamar babban zaki ga Yahuda. Zan yage su kucu-kucu in tafi; zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.

  7. Sa’an nan zan koma wurina sai sun yarda da laifinsu. Za su kuma nemi fuskata; cikin azabansu za su nace da nemana.”

  8. Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa.