Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions Made Beneficial: In keeping us from again departing from God

5 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da In keeping us from again departing from God

  1. “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.

  2. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’

  3. A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  4. Za su ɗauki hakkin laifinsu annabin zai zama mai laifi daidai da wanda ya zo neman shawararsa.

  5. Sa’an nan mutanen Isra’ila ba za su ƙara kauce daga gare ni ba, ba kuwa za su ƙara ƙazantar da kansu da dukan zunubansu ba. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”