Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions Made Beneficial: In purifying us

10 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da In purifying us

  1. Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka.

  2. Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara.

  3. Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki.

  4. Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.”

  5. Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala.

  6. Kai kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji.

  7. Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi zan tace in kuma gwada su, gama me kuwa zan yi saboda zunubin mutanena?

  8. Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”

  9. Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki.

  10. Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci.