Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abraham

314 ayoyi · 39 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.

  2. Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?” Ibrahim ya ce, “Tana can cikin tenti.”

  3. Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.” Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti.

  4. Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa.

  5. Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?”

  6. Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’

  7. Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”

  8. Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.” Ya ce, “A’a, kin yi dariya.”

  9. Sai mutanen suka tashi suka nufi Sodom, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya, ya yi bankwana da su.

  10. Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”

  11. Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta?

  12. Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba?

  13. Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”

  14. Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.”

  15. Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka,

  16. in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.”

  17. Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.”

  18. Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.”

  19. Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.”

  20. Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.”

  21. Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji.

  22. Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya.

  23. Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.”

  24. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.

  25. Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.