Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 26:41kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne kabilan Benyamin, jimillarsu ta kai 45,600.

  2. Ƙidaya 26:42kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne kabilan Dan bisa ga kabilarsu, daga Shuham, kabilar Shuhamawa. Waɗannan su ne kabilan Dan.

  3. Ƙidaya 26:43kusan 1452 K.H.

    Dukansu kabilan Shuhamawa ne, jimillarsu ta kai 64,400.

  4. Ƙidaya 26:44kusan 1452 K.H.

    Zuriyar Asher bisa ga kabilansu, daga Imna, kabilar Imnawa daga Ishbi, kabilar Ishbiyawa; daga Beriya, kabilar Beriyawa;

  5. Ƙidaya 26:45kusan 1452 K.H.

    daga zuriyar Beriya kuwa, daga Heber, kabilar Heberawa; daga Malkiyel, kabilar Malkiyelawa.

  6. Ƙidaya 26:46kusan 1452 K.H.

    (Asher yana da ’ya mace da ake kira Sera.)

  7. Ƙidaya 26:47kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne kabilan Asher; jimillarsu ta kai 53,400.

  8. Ƙidaya 26:48kusan 1452 K.H.

    Zuriyar Naftali bisa ga kabilansu, daga Yazeyel, kabilar Yazeyelawa; daga Guni, kabilar Guniyawa;

  9. Ƙidaya 26:49kusan 1452 K.H.

    daga Yezer, kabilar Yezerawa; daga Shillem, kabilar Shillemawa.

  10. Ƙidaya 26:50kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne kabilan Naftali, jimillarsu ta kai 45,400.

  11. Ƙidaya 26:51kusan 1452 K.H.

    Dukan jimillar mazan Isra’ila ta kai 601,730.

  12. Ƙidaya 26:52kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa,

  13. Ƙidaya 26:53kusan 1452 K.H.

    “Ka rarraba musu ƙasar a matsayin gādo, bisa ga yawan kabila.

  14. Ƙidaya 26:54kusan 1452 K.H.

    Ga ƙungiya mafi girma, ka ba ta rabo mafi girma; ga ƙaramar ƙungiya kuwa, ka ba ta ƙarami rabo; kowane zai karɓa rabonsa ga yawan mutanen da aka rubuta.

  15. Ƙidaya 26:55kusan 1452 K.H.

    Ka tabbatar an rarraba ƙasar ta wurin rabo. Abin da kowace ƙungiya ta gāda zai zama bisa ga sunayen kabilar kakanninta.

  16. Ƙidaya 26:56kusan 1452 K.H.

    Za a raba kowane gādo bisa ga rabo tsakanin manyan da ƙanana ƙungiyoyi.”

  17. Ƙidaya 26:57kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne Lawiyawa da a ƙidaya bisa ga kabilansu, daga Gershom, kabilar Gershonawa; daga Kohat, kabilar Kohatawa; daga Merari, kabilar Merari.

  18. Ƙidaya 26:58kusan 1452 K.H.

    Waɗannan kuma su ne kabilan Lawiyawa, kabilar Libniyawa, kabilar Hebronawa, kabilar Maliyawa, kabilar Mushiyawa, kabilar Korayawa (Kohat shi ne kakan Amram;

  19. Ƙidaya 26:59kusan 1452 K.H.

    sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam.

  20. Ƙidaya 26:60kusan 1452 K.H.

    Haruna shi ne mahaifin Nadab, Abihu, Eleyazar da kuma Itamar.

  21. Ƙidaya 26:61kusan 1452 K.H.

    Amma Nadab da Abihu sun mutu sa’ad da suka miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji.)

  22. Ƙidaya 26:62kusan 1452 K.H.

    Dukan ’ya’yan Lawiyawa maza daga wata ɗaya zuwa gaba, jimillarsu ta kai 23,000. Ba a ƙidaya su tare da sauran Isra’ilawa ba, domin ba a ba su gādo tare da su ba.

  23. Ƙidaya 26:63kusan 1452 K.H.

    Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eleyazar firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a filaye Mowab kusa da Urdun a hayen Yeriko.

  24. Ƙidaya 26:64kusan 1452 K.H.

    Ba ko ɗayansu da yake cikin waɗanda Musa da Haruna firist, suka ƙidaya sa’ad da suka ƙidaya Isra’ilawa a Hamadar Sinai.

  25. Ƙidaya 26:65kusan 1452 K.H.

    Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa waɗancan Isra’ilawa cewa lalle za su mutu a hamada, kuma ba ko ɗayansu da ya rage, sai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.