- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ƙidaya 27:1kusan 1452 K.H.
’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.
- Ƙidaya 27:2kusan 1452 K.H.
Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce,
- Ƙidaya 27:3kusan 1452 K.H.
“Mahaifinmu ya mutu a hamada. Ba ya cikin mabiyan Kora waɗanda suka taru suka tayar wa Ubangiji, amma ya mutu ne saboda zunubinsa, bai kuma bar ’ya’ya maza ba.
- Ƙidaya 27:4kusan 1452 K.H.
Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.”
- Ƙidaya 27:5kusan 1452 K.H.
Saboda haka Musa ya kawo maganarsu a gaban Ubangiji.
- Ƙidaya 27:6kusan 1452 K.H.
Ubangiji kuwa ya ce wa masa,
- Ƙidaya 27:7kusan 1452 K.H.
“Abin da ’ya’yan nan mata na Zelofehad suke faɗi gaskiya ne. Dole ka ba su mallaka a matsayin gādo cikin ’yan’uwan mahaifinsu, ka kuma mayar musu da gādon mahaifinsu.
- Ƙidaya 27:8kusan 1452 K.H.
“Ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘In wani ya mutu ba shi da ɗa, a ba da gādonsa ga ’yarsa.
- Ƙidaya 27:9kusan 1452 K.H.
In ba shi da diya, sai a ba wa ’yan’uwansa gādonsa.
- Ƙidaya 27:10kusan 1452 K.H.
In ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga ’yan’uwan mahaifinsa.
- Ƙidaya 27:11kusan 1452 K.H.
In mahaifinsa ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga danginsa na kusa, a kabilarsa don yă mallaka. Wannan ya zama ƙa’ida wa Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarci Musa.’ ”
- Ƙidaya 27:12kusan 1452 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa wannan dutse a Abarim. Ka ga ƙasar da na ba wa Isra’ilawa.
- Ƙidaya 27:13kusan 1452 K.H.
Bayan ka gani, kai ma za ka bi ƙafafun mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya yi,
- Ƙidaya 27:14kusan 1452 K.H.
gama sa’ad da jama’a suka yi tayarwa saboda rashin ruwa a Hamadan Zin, ku biyu, ba ku kiyaye umarnina don ku ɗaukaka ni matsayin mai tsarki, a gabansu ba.” (Waɗannan su ne ruwaye na Meriba da Kadesh, a Hamadan Zin.)
- Ƙidaya 27:15kusan 1452 K.H.
Musa ya ce wa Ubangiji,
- Ƙidaya 27:16kusan 1452 K.H.
“Bari Ubangiji, Allah na ruhohin ’yan adam, yă naɗa wani a kan wannan jama’a
- Ƙidaya 27:17kusan 1452 K.H.
yă shiga, yă kuma fita a gabansu, wanda zai bishe su zuwa waje, yă kuma dawo da su ciki, don kada mutanen Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyayi.”
- Ƙidaya 27:18kusan 1452 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutumin da ruhun shugabanci yake a cikinsa, ka ɗibiya masa hannunka.
- Ƙidaya 27:19kusan 1452 K.H.
Ka sa yă tsaya a gaban Eleyazar firist, da gaban dukan jama’a, sa’an nan ka keɓe shi a gabansu.
- Ƙidaya 27:20kusan 1452 K.H.
Ka danƙa masa ikonka don dukan jama’a Isra’ilawa su yi masa biyayya.
- Ƙidaya 27:21kusan 1452 K.H.
Zai tsaya a gaban Eleyazar firist, wanda zai nemi masa shawara ta wurin Urim a gaban Ubangiji. Da umarninsa, da shi da dukan jama’ar Isra’ilawa za su fita, da umarninsa kuma za su shiga.”
- Ƙidaya 27:22kusan 1452 K.H.
Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Yoshuwa, ya sa ya tsaya a gaban Eleyazar firist, da kuma gaban dukan jama’a.
- Ƙidaya 27:23kusan 1452 K.H.
Sai ya ɗibiya masa hannuwansa, ya keɓe shi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
- Ƙidaya 28:1kusan 1452 K.H.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
- Ƙidaya 28:2kusan 1452 K.H.
“Ka umarci Isra’ilawa cewa, ‘Ku tabbatar kun miƙa mini hadaya ta abinci ta wuta mai daɗin ƙanshi a gare ni, a daidai lokaci.’