Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 28:3kusan 1452 K.H.

    Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani.

  2. Ƙidaya 28:4kusan 1452 K.H.

    A miƙa rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma,

  3. Ƙidaya 28:5kusan 1452 K.H.

    tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.

  4. Ƙidaya 28:6kusan 1452 K.H.

    Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  5. Ƙidaya 28:7kusan 1452 K.H.

    Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.

  6. Ƙidaya 28:8kusan 1452 K.H.

    Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  7. Ƙidaya 28:9kusan 1452 K.H.

    “ ‘A ranar Asabbaci, za a miƙa ’yan raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya marasa lahani, tare da hadaya ta sha, da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai.

  8. Ƙidaya 28:10kusan 1452 K.H.

    Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha.

  9. Ƙidaya 28:11kusan 1452 K.H.

    “ ‘A rana ta fari ga kowane wata, za a miƙa wa Ubangiji hadayun ’yan bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan tumaki bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu kuma marasa lahani.

  10. Ƙidaya 28:12kusan 1452 K.H.

    Da kowane bijimi, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi uku bisa goma na efa; da ɗan rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi biyu bisa goma na efa;

  11. Ƙidaya 28:13kusan 1452 K.H.

    da kowane tunkiya kuma, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai, na kashi ɗaya bisa goma na efa. Wannan hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  12. Ƙidaya 28:14kusan 1452 K.H.

    Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara.

  13. Ƙidaya 28:15kusan 1452 K.H.

    Ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadaya ta sha, za a miƙa bunsuru ɗaya ga Ubangiji, hadaya ce don zunubi.

  14. Ƙidaya 28:16kusan 1452 K.H.

    “ ‘Za a yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari.

  15. Ƙidaya 28:17kusan 1452 K.H.

    A rana ta goma sha biyar ga wannan wata, za a yi biki; kwana bakwai za a ci burodi marar yisti.

  16. Ƙidaya 28:18kusan 1452 K.H.

    A rana ta farko, za ku yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi na kullum ba.

  17. Ƙidaya 28:19kusan 1452 K.H.

    Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya; dukansu kuma marasa lahani ga Ubangiji.

  18. Ƙidaya 28:20kusan 1452 K.H.

    Da kowane bijimi, a shirya kashi ɗaya bisa uku na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda kuwa, a shirya kashi biyu bisa goma na efan lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;

  19. Ƙidaya 28:21kusan 1452 K.H.

    da kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.

  20. Ƙidaya 28:22kusan 1452 K.H.

    A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.

  21. Ƙidaya 28:23kusan 1452 K.H.

    Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya.

  22. Ƙidaya 28:24kusan 1452 K.H.

    Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha.

  23. Ƙidaya 28:25kusan 1452 K.H.

    A rana ta bakwai, za ku yi tsattsarkan taro, amma ba za a yi aikin da aka saba yi kullum ba.

  24. Ƙidaya 28:26kusan 1452 K.H.

    “ ‘A ranar nunan fari, sa’ad da za ku miƙa wa Ubangiji hadayar sabon hatsi, a lokacin Bikin Makoni, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba.

  25. Ƙidaya 28:27kusan 1452 K.H.

    A miƙa hadaya ta ƙonawa da ’yan bijimai biyu, rago ɗaya da ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.