- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 95
The Revelation
John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ru’uya ta Yohanna 18:5kusan 96 M.
gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.
- Ru’uya ta Yohanna 18:6kusan 96 M.
Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.
- Ru’uya ta Yohanna 18:7kusan 96 M.
Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’
- Ru’uya ta Yohanna 18:8kusan 96 M.
Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.
- Ru’uya ta Yohanna 18:9kusan 96 M.
“Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita.
- Ru’uya ta Yohanna 18:10kusan 96 M.
Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’
- Ru’uya ta Yohanna 18:11kusan 96 M.
“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu
- Ru’uya ta Yohanna 18:12kusan 96 M.
kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;
- Ru’uya ta Yohanna 18:13kusan 96 M.
kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.
- Ru’uya ta Yohanna 18:14kusan 96 M.
“Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’
- Ru’uya ta Yohanna 18:15kusan 96 M.
Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki
- Ru’uya ta Yohanna 18:16kusan 96 M.
su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai!
- Ru’uya ta Yohanna 18:17kusan 96 M.
Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa.
- Ru’uya ta Yohanna 18:18kusan 96 M.
Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’
- Ru’uya ta Yohanna 18:19kusan 96 M.
Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’
- Ru’uya ta Yohanna 18:20kusan 96 M.
“Ki yi murna a kanta, ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka! Ku yi murna, ku manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.”
- Ru’uya ta Yohanna 18:21kusan 96 M.
Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce, “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganin ta ba.
- Ru’uya ta Yohanna 18:22kusan 96 M.
Ba za a ƙara jin ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho a cikinki ba. Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a a cikinki kuma ba. Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa a cikinki kuma ba.
- Ru’uya ta Yohanna 18:23kusan 96 M.
Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.
- Ru’uya ta Yohanna 18:24kusan 96 M.
A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”
- Ru’uya ta Yohanna 19:1kusan 96 M.
Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,
- Ru’uya ta Yohanna 19:2kusan 96 M.
gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.”
- Ru’uya ta Yohanna 19:3kusan 96 M.
Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.”
- Ru’uya ta Yohanna 19:4kusan 96 M.
Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!”
- Ru’uya ta Yohanna 19:5kusan 96 M.
Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!”