Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 95

The Revelation

John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.

404 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su

  2. suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai.

  3. Wane ne ba zai ji tsoronka, yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.”

  4. Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, tabanakul na Shaida, a buɗe.

  5. Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.

  6. Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin.

  7. Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai.

  8. Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”

  9. Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.

  10. Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.

  11. Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini.

  12. Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;

  13. gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”

  14. Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”

  15. Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta.

  16. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.

  17. Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba

  18. suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.

  19. Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas.

  20. Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan.

  21. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

  22. “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”

  23. Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.

  24. Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!”

  25. Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce.