Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 95

The Revelation

John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.

404 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.

  2. Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

  3. Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)

  4. Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”

  5. Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”

  6. Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.

  7. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi.

  8. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.

  9. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.

  10. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.

  11. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.

  12. Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah,

  13. don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”

  14. Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa.

  15. Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci.

  16. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.

  17. Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa.

  18. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.

  19. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.

  20. Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.

  21. (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.

  22. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.

  23. Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake,

  24. zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.

  25. Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.