Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 8:20kusan 32 M.

    “Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka ce, “Bakwai.”

  2. Markus 8:21kusan 32 M.

    Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”

  3. Markus 8:22kusan 32 M.

    Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi.

  4. Markus 8:23kusan 32 M.

    Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”

  5. Markus 8:24kusan 32 M.

    Sai ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.”

  6. Markus 8:25kusan 32 M.

    Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai.

  7. Markus 8:26kusan 32 M.

    Yesu ya sallame shi gida ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen.”

  8. Markus 8:27kusan 32 M.

    Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”

  9. Markus 8:28kusan 32 M.

    Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Iliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.”

  10. Markus 8:29kusan 32 M.

    Sai ya yi tambaya ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi.”

  11. Markus 8:30kusan 32 M.

    Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa.

  12. Markus 8:31kusan 32 M.

    Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi.

  13. Markus 8:32kusan 32 M.

    Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsawata masa.

  14. Markus 8:33kusan 32 M.

    Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da al’amuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”

  15. Markus 8:34kusan 32 M.

    Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.

  16. Markus 8:35kusan 32 M.

    Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.

  17. Markus 8:36kusan 32 M.

    Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?

  18. Markus 8:37kusan 32 M.

    Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?

  19. Markus 8:38kusan 32 M.

    Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”

  20. Markus 9:1kusan 32 M.

    Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”

  21. Markus 9:2kusan 32 M.

    Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.

  22. Markus 9:3kusan 32 M.

    Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.

  23. Markus 9:4kusan 32 M.

    Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  24. Markus 9:5kusan 32 M.

    Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

  25. Markus 9:6kusan 32 M.

    (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)