Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 7:32kusan 32 M.

    A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin.

  2. Markus 7:33kusan 32 M.

    Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin.

  3. Markus 7:34kusan 32 M.

    Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”).

  4. Markus 7:35kusan 32 M.

    Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.

  5. Markus 7:36kusan 32 M.

    Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi.

  6. Markus 7:37kusan 32 M.

    Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”

  7. Markus 8:1kusan 32 M.

    A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce,

  8. Markus 8:2kusan 32 M.

    “Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci.

  9. Markus 8:3kusan 32 M.

    In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”

  10. Markus 8:4kusan 32 M.

    Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”

  11. Markus 8:5kusan 32 M.

    Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”

  12. Markus 8:6kusan 32 M.

    Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka.

  13. Markus 8:7kusan 32 M.

    Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu.

  14. Markus 8:8kusan 32 M.

    Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai.

  15. Markus 8:9kusan 32 M.

    Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su,

  16. Markus 8:10kusan 32 M.

    sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.

  17. Markus 8:11kusan 32 M.

    Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yă nuna musu wata alama daga sama.

  18. Markus 8:12kusan 32 M.

    Sai ya ja numfashi mai zurfi ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.”

  19. Markus 8:13kusan 32 M.

    Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin.

  20. Markus 8:14kusan 32 M.

    Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan.

  21. Markus 8:15kusan 32 M.

    Yesu ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”

  22. Markus 8:16kusan 32 M.

    Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”

  23. Markus 8:17kusan 32 M.

    Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?

  24. Markus 8:18kusan 32 M.

    Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba?

  25. Markus 8:19kusan 32 M.

    Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka amsa, “Sha biyu.”