Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 6:38kusan 28 M.

    Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”

  2. Markus 6:39kusan 28 M.

    Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.

  3. Markus 6:40kusan 28 M.

    Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.

  4. Markus 6:41kusan 28 M.

    Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.

  5. Markus 6:42kusan 28 M.

    Kowa ya ci, ya ƙoshi,

  6. Markus 6:43kusan 28 M.

    almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.

  7. Markus 6:44kusan 28 M.

    Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.

  8. Markus 6:45kusan 28 M.

    Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron.

  9. Markus 6:46kusan 28 M.

    Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.

  10. Markus 6:47kusan 28 M.

    Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.

  11. Markus 6:48kusan 28 M.

    Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,

  12. Markus 6:49kusan 28 M.

    amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu,

  13. Markus 6:50kusan 28 M.

    domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

  14. Markus 6:51kusan 28 M.

    Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,

  15. Markus 6:52kusan 28 M.

    gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.

  16. Markus 6:53kusan 28 M.

    Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya.

  17. Markus 6:54kusan 28 M.

    Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.

  18. Markus 6:55kusan 28 M.

    Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.

  19. Markus 6:56kusan 28 M.

    Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.

  20. Markus 7:1kusan 32 M.

    Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu.

  21. Markus 7:2kusan 32 M.

    Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba.

  22. Markus 7:3kusan 32 M.

    (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce.

  23. Markus 7:4kusan 32 M.

    Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)

  24. Markus 7:5kusan 32 M.

    Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”

  25. Markus 7:6kusan 32 M.

    Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.