Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 5:31kusan 31 M.

    Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”

  2. Markus 5:32kusan 31 M.

    Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi.

  3. Markus 5:33kusan 31 M.

    Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru.

  4. Markus 5:34kusan 31 M.

    Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”

  5. Markus 5:35kusan 31 M.

    Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”

  6. Markus 5:36kusan 31 M.

    Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”

  7. Markus 5:37kusan 31 M.

    Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub.

  8. Markus 5:38kusan 31 M.

    Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa.

  9. Markus 5:39kusan 31 M.

    Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.”

  10. Markus 5:40kusan 31 M.

    Sai suka yi masa dariya. Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take.

  11. Markus 5:41kusan 31 M.

    Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”).

  12. Markus 5:42kusan 31 M.

    Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai.

  13. Markus 5:43kusan 31 M.

    Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yă san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.

  14. Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.

  15. Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka!

  16. Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

  17. Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”

  18. Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.

  19. Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.

  20. Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.

  21. Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku.

  22. Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.

  23. Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin.

  24. In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”

  25. Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba.