Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 5:6kusan 31 M.

    Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa.

  2. Markus 5:7kusan 31 M.

    Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!”

  3. Markus 5:8kusan 31 M.

    Gama Yesu ya riga ya ce masa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”

  4. Markus 5:9kusan 31 M.

    Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.”

  5. Markus 5:10kusan 31 M.

    Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin.

  6. Markus 5:11kusan 31 M.

    A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo.

  7. Markus 5:12kusan 31 M.

    Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.”

  8. Markus 5:13kusan 31 M.

    Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.

  9. Markus 5:14kusan 31 M.

    Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru.

  10. Markus 5:15kusan 31 M.

    Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro.

  11. Markus 5:16kusan 31 M.

    Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun.

  12. Markus 5:17kusan 31 M.

    Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu.

  13. Markus 5:18kusan 31 M.

    Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi.

  14. Markus 5:19kusan 31 M.

    Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”

  15. Markus 5:20kusan 31 M.

    Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.

  16. Markus 5:21kusan 31 M.

    Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin.

  17. Markus 5:22kusan 31 M.

    Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa,

  18. Markus 5:23kusan 31 M.

    ya roƙe shi da gaske ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.”

  19. Markus 5:24kusan 31 M.

    Sai Yesu ya tafi tare da shi. Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.

  20. Markus 5:25kusan 31 M.

    A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini.

  21. Markus 5:26kusan 31 M.

    Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni.

  22. Markus 5:27kusan 31 M.

    Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa,

  23. Markus 5:28kusan 31 M.

    domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.”

  24. Markus 5:29kusan 31 M.

    Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.

  25. Markus 5:30kusan 31 M.

    Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”