circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Markus 3:32kusan 31 M.
Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.”
- Markus 3:33kusan 31 M.
Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?”
- Markus 3:34kusan 31 M.
Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana!
- Markus 3:35kusan 31 M.
Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”
- Markus 4:1kusan 31 M.
Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a ciki a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan.
- Markus 4:2kusan 31 M.
Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce,
- Markus 4:3kusan 31 M.
“Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.
- Markus 4:4kusan 31 M.
Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su.
- Markus 4:5kusan 31 M.
Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi.
- Markus 4:6kusan 31 M.
Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa.
- Markus 4:7kusan 31 M.
Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba.
- Markus 4:8kusan 31 M.
Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”
- Markus 4:9kusan 31 M.
Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
- Markus 4:10kusan 31 M.
Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan.
- Markus 4:11kusan 31 M.
Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai.
- Markus 4:12kusan 31 M.
Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”
- Markus 4:13kusan 31 M.
Sai Yesu ya ce musu, “Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan?
- Markus 4:14kusan 31 M.
Manomi yakan shuka maganar Allah.
- Markus 4:15kusan 31 M.
Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.
- Markus 4:16kusan 31 M.
Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.
- Markus 4:17kusan 31 M.
Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.
- Markus 4:18kusan 31 M.
Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar,
- Markus 4:19kusan 31 M.
amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani.
- Markus 4:20kusan 31 M.
Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”
- Markus 4:21kusan 31 M.
Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba?