circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Markus 2:10kusan 31 M.
Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen,
- Markus 2:11kusan 31 M.
“Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”
- Markus 2:12kusan 31 M.
Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”
- Markus 2:13kusan 31 M.
Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu.
- Markus 2:14kusan 31 M.
Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.
- Markus 2:15kusan 31 M.
Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi.
- Markus 2:16kusan 31 M.
Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
- Markus 2:17kusan 31 M.
Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
- Markus 2:18kusan 31 M.
To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?”
- Markus 2:19kusan 31 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su.
- Markus 2:20kusan 31 M.
Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.
- Markus 2:21kusan 31 M.
“Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni.
- Markus 2:22kusan 31 M.
Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”
- Markus 2:23kusan 31 M.
Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi.
- Markus 2:24kusan 31 M.
Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?”
- Markus 2:25kusan 31 M.
Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata?
- Markus 2:26kusan 31 M.
Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”
- Markus 2:27kusan 31 M.
Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba.
- Markus 2:28kusan 31 M.
Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.”
- Markus 3:1kusan 31 M.
Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu.
- Markus 3:2kusan 31 M.
Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.
- Markus 3:3kusan 31 M.
Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”
- Markus 3:4kusan 31 M.
Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.
- Markus 3:5kusan 31 M.
Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
- Markus 3:6kusan 31 M.
Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu.