circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Markus 9:32kusan 32 M.
Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
- Markus 9:33kusan 32 M.
Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”
- Markus 9:34kusan 32 M.
Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
- Markus 9:35kusan 32 M.
Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”
- Markus 9:36kusan 32 M.
Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu,
- Markus 9:37kusan 32 M.
“Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
- Markus 9:38kusan 32 M.
Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”
- Markus 9:39kusan 32 M.
Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni.
- Markus 9:40kusan 32 M.
Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
- Markus 9:41kusan 32 M.
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
- Markus 9:42kusan 32 M.
“Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.
- Markus 9:43kusan 32 M.
In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.
- Markus 9:44kusan 32 M.
Where their worm dieth not, and the fire is not quenched.
- Markus 9:45kusan 32 M.
In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.
- Markus 9:46kusan 32 M.
Where their worm dieth not, and the fire is not quenched.
- Markus 9:47kusan 32 M.
In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu,
- Markus 9:48kusan 32 M.
inda “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’
- Markus 9:49kusan 32 M.
Za a tsarkake kowa da wuta.
- Markus 9:50kusan 32 M.
“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
- Markus 10:1kusan 29 M.
Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.
- Markus 10:2kusan 29 M.
Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”
- Markus 10:3kusan 29 M.
Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”
- Markus 10:4kusan 29 M.
Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”
- Markus 10:5kusan 29 M.
Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka.
- Markus 10:6kusan 29 M.
Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’