Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 10:7kusan 29 M.

    ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,

  2. Markus 10:8kusan 29 M.

    su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.

  3. Markus 10:9kusan 29 M.

    Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”

  4. Markus 10:10kusan 29 M.

    Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan.

  5. Markus 10:11kusan 29 M.

    Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki.

  6. Markus 10:12kusan 29 M.

    In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

  7. Markus 10:13kusan 29 M.

    Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su.

  8. Markus 10:14kusan 29 M.

    Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.

  9. Markus 10:15kusan 29 M.

    Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

  10. Markus 10:16kusan 29 M.

    Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.

  11. Markus 10:17kusan 29 M.

    Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”

  12. Markus 10:18kusan 29 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.

  13. Markus 10:19kusan 29 M.

    Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”

  14. Markus 10:20kusan 29 M.

    Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”

  15. Markus 10:21kusan 29 M.

    Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

  16. Markus 10:22kusan 29 M.

    Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

  17. Markus 10:23kusan 29 M.

    Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”

  18. Markus 10:24kusan 29 M.

    Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!

  19. Markus 10:25kusan 29 M.

    Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

  20. Markus 10:26kusan 29 M.

    Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?”

  21. Markus 10:27kusan 29 M.

    Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”

  22. Markus 10:28kusan 29 M.

    Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!”

  23. Markus 10:29kusan 29 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,

  24. Markus 10:30kusan 29 M.

    sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.

  25. Markus 10:31kusan 29 M.

    Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.”