circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Markus 11:5kusan 33 M.
sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”
- Markus 11:6kusan 33 M.
Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.
- Markus 11:7kusan 33 M.
Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.
- Markus 11:8kusan 33 M.
Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki.
- Markus 11:9kusan 33 M.
Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”
- Markus 11:10kusan 33 M.
“Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”
- Markus 11:11kusan 33 M.
Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
- Markus 11:12kusan 33 M.
Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.
- Markus 11:13kusan 33 M.
Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne.
- Markus 11:14kusan 33 M.
Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
- Markus 11:15kusan 33 M.
Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,
- Markus 11:16kusan 33 M.
ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki.
- Markus 11:17kusan 33 M.
Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’”
- Markus 11:18kusan 33 M.
Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
- Markus 11:19kusan 33 M.
Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin.
- Markus 11:20kusan 33 M.
Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa.
- Markus 11:21kusan 33 M.
Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
- Markus 11:22kusan 33 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah.
- Markus 11:23kusan 33 M.
Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.
- Markus 11:24kusan 33 M.
Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
- Markus 11:25kusan 33 M.
A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”
- Markus 11:26kusan 33 M.
But if ye do not forgive, neither will your Father which is in heaven forgive your trespasses.
- Markus 11:27kusan 33 M.
Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.
- Markus 11:28kusan 33 M.
Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
- Markus 11:29kusan 33 M.
Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.