Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 18:10kusan 33 M.

    Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.)

  2. Yohanna 18:11kusan 33 M.

    Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”

  3. Yohanna 18:12kusan 33 M.

    Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma ma’aikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka daure shi

  4. Yohanna 18:13kusan 33 M.

    sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan.

  5. Yohanna 18:14kusan 33 M.

    Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane.

  6. Yohanna 18:15kusan 33 M.

    Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin,

  7. Yohanna 18:16kusan 33 M.

    Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus.

  8. Yohanna 18:17kusan 33 M.

    Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?” Bitrus ya amsa ya ce, “A’a, ba na ciki.”

  9. Yohanna 18:18kusan 33 M.

    To, ana sanyi, bayi da ma’aikatan suna tsattsaye kewaye da wutar da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi.

  10. Yohanna 18:19kusan 33 M.

    Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.

  11. Yohanna 18:20kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba.

  12. Yohanna 18:21kusan 33 M.

    Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.”

  13. Yohanna 18:22kusan 33 M.

    Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”

  14. Yohanna 18:23kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?”

  15. Yohanna 18:24kusan 33 M.

    Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist.

  16. Yohanna 18:25kusan 33 M.

    Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?” Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.”

  17. Yohanna 18:26kusan 33 M.

    Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?”

  18. Yohanna 18:27kusan 33 M.

    Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara.

  19. Yohanna 18:28kusan 33 M.

    Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa.

  20. Yohanna 18:29kusan 33 M.

    Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?”

  21. Yohanna 18:30kusan 33 M.

    Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.”

  22. Yohanna 18:31kusan 33 M.

    Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.” Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.”

  23. Yohanna 18:32kusan 33 M.

    Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi.

  24. Yohanna 18:33kusan 33 M.

    Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”

  25. Yohanna 18:34kusan 33 M.

    Yesu ya yi tambaya ya ce, “Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”