- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ishaya 9:1kusan 740 K.H.
Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.
- Ishaya 9:2kusan 740 K.H.
Mutanen da suke tafiya cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa haske ya haskaka.
- Ishaya 9:3kusan 740 K.H.
Ka fadada al’umma ka kuma ƙara farin cikinsu; suna farin ciki a gabanka yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi, kamar yadda mutane sukan yi farin ciki sa’ad da suke raba ganima.
- Ishaya 9:4kusan 740 K.H.
Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi, kuka ji tsoro nauyin da ya nawaita musu, sandar da yake a kafaɗunsu, sandar masu zaluncinsu.
- Ishaya 9:5kusan 740 K.H.
Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini zai kasance an ƙone shi zai kuma zama abin hura wuta.
- Ishaya 9:6kusan 740 K.H.
Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama.
- Ishaya 9:7kusan 740 K.H.
Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
- Ishaya 9:8kusan 740 K.H.
Ubangiji ya aika da saƙon gāba da Yaƙub; zai auka wa Isra’ila.
- Ishaya 9:9kusan 740 K.H.
Dukan mutane za su san shi, Efraim da mazaunan Samariya, waɗanda suke magana da fariya suna kuma ɗaga kai,
- Ishaya 9:10kusan 740 K.H.
“Tubalai sun zube a ƙasa, amma za mu sāke gina su da dutse; an sassare itatuwan ɓaure, amma za mu maya su da al’ul.”
- Ishaya 9:11kusan 740 K.H.
Amma Ubangiji ya ƙarfafa maƙiyan Rezin gāba da su ya kuma ingiza abokan gāba.
- Ishaya 9:12kusan 740 K.H.
Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
- Ishaya 9:13kusan 740 K.H.
Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba, balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.
- Ishaya 9:14kusan 740 K.H.
Saboda haka Ubangiji zai yanke Isra’ila kai da wutsiya, da reshen dabino da iwa a rana guda;
- Ishaya 9:15kusan 740 K.H.
dattawa da manyan mutane su ne kai, annabawa waɗanda suke koyar da ƙarairayi su ne wutsiya.
- Ishaya 9:16kusan 740 K.H.
Waɗanda suke jagorar wannan mutane suna ɓad da su, su ne waɗanda ake jagora aka sa suka kauce.
- Ishaya 9:17kusan 740 K.H.
Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba, ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba, gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu, kowane baki yana faɗin mugayen maganganu. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
- Ishaya 9:18kusan 740 K.H.
Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta; tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya, ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa, don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama.
- Ishaya 9:19kusan 740 K.H.
Ta wurin fushin Ubangiji Maɗaukaki ƙasar za tă ci wuta mutane kuma za su zama abin hura wutar, babu wanda zai ji tausayin ɗan’uwansa.
- Ishaya 9:20kusan 740 K.H.
A dama za su ci, amma su ci gaba da jin yunwa; a hagu za su ci, amma ba za su ƙoshi ba. Kowa zai mai da naman ’ya’yansa abinci.
- Ishaya 9:21kusan 740 K.H.
Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse; tare za su yi gāba da Yahuda. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
- Ishaya 10:1kusan 713 K.H.
Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya, waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,
- Ishaya 10:2kusan 713 K.H.
don su hana matalauta hakkinsu su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena, suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu suna kuma yi wa marayu ƙwace.
- Ishaya 10:3kusan 713 K.H.
Me za ku yi a ranan nan ta hukunci, sa’ad da masifa ta zo daga nesa? Ga wa za ku tafi don neman taimako? Ina za ku bar dukiyarku?
- Ishaya 10:4kusan 713 K.H.
Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.