Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 6:11kusan 759 K.H.

    Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,

  2. Ishaya 6:12kusan 759 K.H.

    sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.

  3. Ishaya 6:13kusan 759 K.H.

    Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar, za tă sāke zama kango. Amma kamar yadda katambiri da itacen oak sukan bar kututturai sa’ad da aka yanke su, haka iri mai tsarkin nan zai zama kututture a ƙasar mai tsarki.”

  4. Ishaya 7:1kusan 741 K.H.

    Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.

  5. Ishaya 7:2kusan 741 K.H.

    Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.

  6. Ishaya 7:3kusan 741 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.

  7. Ishaya 7:4kusan 741 K.H.

    Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.

  8. Ishaya 7:5kusan 741 K.H.

    Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa,

  9. Ishaya 7:6kusan 741 K.H.

    “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.”

  10. Ishaya 7:7kusan 741 K.H.

    Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “ ‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba,

  11. Ishaya 7:8kusan 741 K.H.

    gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.

  12. Ishaya 7:9kusan 741 K.H.

    Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ”

  13. Ishaya 7:10kusan 741 K.H.

    Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce,

  14. Ishaya 7:11kusan 741 K.H.

    “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”

  15. Ishaya 7:12kusan 741 K.H.

    Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”

  16. Ishaya 7:13kusan 741 K.H.

    Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure?

  17. Ishaya 7:14kusan 741 K.H.

    Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.

  18. Ishaya 7:15kusan 741 K.H.

    In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.

  19. Ishaya 7:16kusan 741 K.H.

    Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango.

  20. Ishaya 7:17kusan 741 K.H.

    Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”

  21. Ishaya 7:18kusan 741 K.H.

    A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya.

  22. Ishaya 7:19kusan 741 K.H.

    Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.

  23. Ishaya 7:20kusan 741 K.H.

    A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.

  24. Ishaya 7:21kusan 741 K.H.

    A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai.

  25. Ishaya 7:22kusan 741 K.H.

    Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.