- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 605–538 BC
The Babylonian Exile
Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ezekiyel 42:9kusan 574 K.H.
Ɗakunan da suke can ƙasa suna da ƙofar shiga a wajen gabas in za a shiga cikinsu daga filin da yake waje.
- Ezekiyel 42:10kusan 574 K.H.
A wajen kudu a ta katangar filin da yake waje, kusa da filin haikali da yake ɗaura da katangar waje, akwai ɗakuna
- Ezekiyel 42:11kusan 574 K.H.
da hanya a gabansu. Waɗannan sun yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa; tsawonsu da fāɗinsu duk iri ɗaya ne, da irin mafita ɗaya da kuma yadda aka shirya su. Sun yi kama da ƙofofin da suke wajen arewa
- Ezekiyel 42:12kusan 574 K.H.
haka ma ƙofofin ɗakunan a wajen kudu. Akwai ƙofa a farkon hanyar da ta yi hannun riga da ɗayan katangar da ta miƙe wajen gabas, inda za a iya shiga ɗakunan.
- Ezekiyel 42:13kusan 574 K.H.
Sai ya ce mini, “Ɗakunan arewa da na kudu waɗanda suke fuskantar filin haikali ɗakunan firistoci ne, inda firistocin da suke kusaci Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A can za su ajiye hadayu mafi tsarki, hadayu na gari, hadayu na zunubi da hadayu na laifi, gama wuri mai tsarki ne.
- Ezekiyel 42:14kusan 574 K.H.
Da zarar firistoci suka shiga wuri mai tsarki, ba za su fita zuwa filin da yake waje ba sai sun tuɓe rigunan da suka yi hidima da su, gama waɗannan masu tsarki ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su kusaci wuraren da mutane suke.”
- Ezekiyel 42:15kusan 574 K.H.
Da ya gama auna filin da yake cikin haikali, sai ya fitar da ni ta ƙofar gabas ya auna dukan filin kewaye.
- Ezekiyel 42:16kusan 574 K.H.
Ya auna gefen gabas da karan awo; ya samu kamu ɗari biyar.
- Ezekiyel 42:17kusan 574 K.H.
Ya auna gefen arewa da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.
- Ezekiyel 42:18kusan 574 K.H.
Ya auna gefen kudu da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.
- Ezekiyel 42:19kusan 574 K.H.
Sa’an nan ya juya zuwa gefen yamma ya auna shi da karan awon, ya samu kamu ɗari biya.
- Ezekiyel 42:20kusan 574 K.H.
Ta haka ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana da katanga kewaye da shi, tsawon kamu ɗari biyar, fāɗin kuma kamu ɗari biyar don yă raba wuri mai tsarki daga wuri marar tsarki.
- Ezekiyel 43:1kusan 574 K.H.
Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da take fuskantar gabas,
- Ezekiyel 43:2kusan 574 K.H.
sai na ga ɗaukakar Allah na Isra’ila tana tahowa daga gabas. Muryarsa ta yi kamar rurin ruwaye masu gudu, ƙasa kuma ta haskaka da ɗaukakarsa.
- Ezekiyel 43:3kusan 574 K.H.
Wahayin da na gani ya yi kamar wahayin da na gani sa’ad da ya zo don yă hallaka birnin, kamar kuma wahayin da na gani kusa da Kogin Kebar, na kuwa fāɗi rubda ciki.
- Ezekiyel 43:4kusan 574 K.H.
Ɗaukakar Ubangiji ta shiga haikali ta ƙofar da take fuskantar gabas.
- Ezekiyel 43:5kusan 574 K.H.
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin fili na can ciki, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
- Ezekiyel 43:6kusan 574 K.H.
Yayinda mutumin yana tsaye kusa da ni, na ji wani yana magana da ni daga cikin haikalin.
- Ezekiyel 43:7kusan 574 K.H.
Ya ce, “Ɗan mutum, wannan shi ne kursiyina da wurin tafin ƙafafuna. A nan ne zan zauna a cikin Isra’ilawa har abada. Gidan Isra’ila ba zai ƙara ɓata sunana mai tsarki ba, ko su ko sarakunansu, ta wurin karuwanci da gumakan da ba su da rai, sarakunansu a masujadan kan tudu.
- Ezekiyel 43:8kusan 574 K.H.
Sa’ad da suka sa madogarar ƙofarsu kusa da madogarar ƙofata, da katanga kawai a tsakanina da su, sun ɓata sunana mai tsarki ta wurin ayyukansu masu banƙyama. Saboda haka na hallaka su cikin fushina.
- Ezekiyel 43:9kusan 574 K.H.
Yanzu bari su kawar da karuwancinsu da gumakansu waɗanda ba su da rai na sarakunansu daga gabana, zan kuwa zauna a cikinsu har abada.
- Ezekiyel 43:10kusan 574 K.H.
“Ɗan mutum, ka bayyana haikalin ga mutanen Isra’ila, don su ji kunya saboda zunubansu. Bari su yi la’akari da fasalin,
- Ezekiyel 43:11kusan 574 K.H.
kuma in suka ji kunyar abubuwan da suka aikata, sai ka sanar musu fasalin haikalin da shirye-shiryensa, ƙofofinsa na shiga da fita, dukan fasalinsa da dukan ƙa’idodinsa da dokokinsa. Ka rubuta waɗannan a gabansu saboda su yi aminci da fasalinsa su kuma kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
- Ezekiyel 43:12kusan 574 K.H.
“Wannan ita ce dokar haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, zai zama wuri mafi tsarki. Dokar haikalin ke nan.
- Ezekiyel 43:13kusan 574 K.H.
“Waɗannan su ne aune-aunen bagade a tsawon kamu, wannan kamu shi ne kamun tafin hannu. Zurfin magudanar ruwansa kamu ɗaya ne fāɗinsa kuma kamu ɗaya, tare da da’ira kamun tafi ɗaya kewaye da gefensa. Wannan kuma shi ne tsayin bagaden.