Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ezekiyel 40:34kusan 574 K.H.

    Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogararta. Tana kuma da matakai takwas.

  2. Ezekiyel 40:35kusan 574 K.H.

    Sa’an nan ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta. Girmanta ɗaya ne da sauran,

  3. Ezekiyel 40:36kusan 574 K.H.

    Haka ma ɗakunanta, bangayenta da shirayinta, ƙofar tana da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

  4. Ezekiyel 40:37kusan 574 K.H.

    Shirayin ƙofar ta fuskanci filin waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogaranta, matakai takwas kuwa sun haura zuwa wajenta.

  5. Ezekiyel 40:38kusan 574 K.H.

    Ɗakin da hanya ta ratsa ciki yana kusa da shirayin a kowane hanyoyin shiga na ciki, inda a kan wanke hadayun ƙonawa.

  6. Ezekiyel 40:39kusan 574 K.H.

    A shirayin hanyar shiga akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yankan hadayun ƙonawa, hadayun zunubi da kuma hadayun laifi.

  7. Ezekiyel 40:40kusan 574 K.H.

    Ta bangon waje na shirayin hanyar shiga, kusa da matakai a mashigin zuwa hanyar shiga da take arewa akwai tebur biyu, akwai kuma tebur biyu a gefe ɗaya na matakan.

  8. Ezekiyel 40:41kusan 574 K.H.

    Duka dai akwai tebur huɗu a gefe ɗaya na hanyar shiga, huɗu kuma a ɗaya gefen, tebur takwas ke nan gaba ɗaya, inda a kan yanka hadayu a kai.

  9. Ezekiyel 40:42kusan 574 K.H.

    Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu don hadayun ƙonawa, tsawon kowanne kuwa kamu ɗaya da rabi ne, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya. A kansu ne a kan ajiye kayan yanka hadayun ƙonawa da kuma sauran hadayu.

  10. Ezekiyel 40:43kusan 574 K.H.

    Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye a bangon, tsawon kowanne ya yi fāɗin tafin hannu. An yi amfani da teburin don a riƙa ajiye naman hadayu.

  11. Ezekiyel 40:44kusan 574 K.H.

    Waje da ƙofar ciki, a cikin filin ciki, akwai ɗakuna biyu, ɗaya a gefen ƙofar arewa yana kuma fuskantar kudu, wani kuma a gefen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.

  12. Ezekiyel 40:45kusan 574 K.H.

    Sai mutumin ya ce mini, “Ɗakin da yake fuskantar kudu ne na firistocin da suke lura da haikali,

  13. Ezekiyel 40:46kusan 574 K.H.

    ɗaya ɗakin kuma da yake fuskantar arewa ne na firistocin da suke lura da bagade. Waɗannan su ne ’ya’yan Zadok maza, waɗanda su ne kaɗai Lawiyawan da za su iya yin kusa da Ubangiji don su yi hidima a gabansa.”

  14. Ezekiyel 40:47kusan 574 K.H.

    Sa’an nan ya auna filin, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu ɗari. Bagaden kuwa yana a gaba a cikin haikalin.

  15. Ezekiyel 40:48kusan 574 K.H.

    Sai ya kawo ni shirayin haikalin ya kuma auna madogaran shirayin; fāɗinsu a kowane gefe kamu biyar-biyar ne. Fāɗin mashigin kamu goma sha huɗu ne, bangayenta kuma kamu uku-uku ne a kowane gefe.

  16. Ezekiyel 40:49kusan 574 K.H.

    Fāɗin shirayin kamu ashirin ne, kamu goma sha biyu kuma daga gaba zuwa baya. A kan kai samansa ta wurin hawan matakai, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe na madogaran.

  17. Ezekiyel 41:1kusan 574 K.H.

    Sai mutumin ya kawo ni wuri mai tsarki da yake waje ya kuma auna madogaransa; fāɗin gefe-gefen kamu shida ne a kowane gefe.

  18. Ezekiyel 41:2kusan 574 K.H.

    Faɗin ƙofar shiga kamu goma ne, fāɗin bangaye a kowane madogararta kamu biyar-biyar ne. Ya kuma auna wuri mai tsarkin da yake waje; tsawonsa kamu arba’in fāɗinsa kuma kamu ashirin.

  19. Ezekiyel 41:3kusan 574 K.H.

    Sa’an nan ya shiga wuri mai tsarki da yake can ciki ya auna madogarar ƙofar shigar; fāɗin kowanne kamu biyu ne. Faɗin ƙofar shigan kamu shida ne, fāɗin bangayen a kowane gefenta kamu bakwai-bakwai ne.

  20. Ezekiyel 41:4kusan 574 K.H.

    Ya kuma auna tsawon wuri mai tsarki da yake can ciki; tsawon kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin daga ƙurewa wuri mai tsarki da yake waje. Ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”

  21. Ezekiyel 41:5kusan 574 K.H.

    Sa’an nan ya auna bangon haikalin; kaurinsa kamu shida ne, kuma kowane ɗakin da yake a gefe kewaye da haikalin fāɗinsa kamu huɗu ne.

  22. Ezekiyel 41:6kusan 574 K.H.

    Ɗakunan da suke gefe masu hawa uku ne, wani bisa wani, guda talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da bangayen haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon haikalin.

  23. Ezekiyel 41:7kusan 574 K.H.

    Faɗin ɗakunan da suke gefe kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. Ginin da aka yi kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, don haka ɗakunan suka yi ta ƙara fāɗi yayinda suka ƙara bisa. Akwai mataki daga ɗaki na ƙasa zuwa ɗaki na bisa ta hanya hawa ɗaki na tsakiya.

  24. Ezekiyel 41:8kusan 574 K.H.

    Na ga cewa haikalin yana da ɗagaggen tushe kewaye da shi, wanda ya zama harsashin ɗakunan da suke gefe. Tsawonsa kara guda ne mai tsawon kamu shida.

  25. Ezekiyel 41:9kusan 574 K.H.

    Kaurin bangon waje na ɗakunan da suke gefe kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan da suke gefen haikalin