- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Moses & The Exodus
God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 4:7kusan 1491 K.H.
Sai Ubangiji ya ce, “Yanzu, mayar da hannunka a rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, da ya fitar da shi, sai hannun ya koma kamar sauran jikinsa.
- Fitowa 4:8kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “In ba su gaskata ba, ko kuma ba su kula da mu’ujiza ta fari ba, wataƙila su gaskata da ta biyun.
- Fitowa 4:9kusan 1491 K.H.
Amma in ba su gaskata mu’ujizan nan biyu ba, ko kuwa ba su saurare ka ba, sai ka ɗibo ruwa daga Nilu, ka zuba a busasshiyar ƙasa. Ruwan da ka ɗebo daga kogin zai zama jini a ƙasar.”
- Fitowa 4:10kusan 1491 K.H.
Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”
- Fitowa 4:11kusan 1491 K.H.
Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne?
- Fitowa 4:12kusan 1491 K.H.
Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.”
- Fitowa 4:13kusan 1491 K.H.
Amma Musa ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka nemi wani ka aika.”
- Fitowa 4:14kusan 1491 K.H.
Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka.
- Fitowa 4:15kusan 1491 K.H.
Za ka yi masa magana. Ka kuma sa masa maganata a baki; zan kuma taimake ku magana, in koya muku abin da za ku yi.
- Fitowa 4:16kusan 1491 K.H.
Zai yi magana da mutane a madadinka, zai zama kamar bakinka, kai kuwa kamar Allah a gare shi.
- Fitowa 4:17kusan 1491 K.H.
Amma ka ɗauki wannan sanda a hannunka domin yă aikata mu’ujizan.”
- Fitowa 4:18kusan 1491 K.H.
Sai Musa ya koma wurin Yetro surukinsa, ya ce masa, “Bari in koma wurin mutanena a Masar, in ga ko da mai rai a cikinsu.” Yetro ya ce, “Tafi, ka kuma sauka lafiya.”
- Fitowa 4:19kusan 1491 K.H.
Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa a Midiyan, “Koma Masar, domin dukan mutanen da suke neman su kashe ka sun mutu.”
- Fitowa 4:20kusan 1491 K.H.
Sai Musa ya ɗauki matarsa da ’ya’yansa maza, ya sa su a kan jaki, suka kama hanya zuwa Masar. Ya kuma ɗauki sandan Allah a hannunsa.
- Fitowa 4:21kusan 1491 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Bayan ka koma Masar, ka tabbata ka aikata dukan mu’ujizan da na sa cikin ikonka a gaban Fir’auna. Amma zan taurare zuciyarsa domin kada yă bar mutanen su tafi.
- Fitowa 4:22kusan 1491 K.H.
Sa’an nan ka gaya wa Fir’auna, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce; Isra’ila shi ne ɗan farina,
- Fitowa 4:23kusan 1491 K.H.
na gaya maka, “Ka bar ɗana yă tafi domin yă yi mini sujada.” Amma ka ƙi ka bari yă tafi, saboda haka zan kashe ɗan farinka.’ ”
- Fitowa 4:24kusan 1491 K.H.
Ya zama kuwa sa’ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi.
- Fitowa 4:25kusan 1491 K.H.
Amma Ziffora ta ɗauki dutsen ƙanƙara mai ci, ta yanke loɓar ɗanta ta taɓa ƙafafun Musa da shi. Ta ce, “Tabbatacce kai angon jini ne a gare ni.”
- Fitowa 4:26kusan 1491 K.H.
Sai Ubangiji ya ƙyale shi. (A lokacin ta ce “angon jini,” tana nufin kaciya.)
- Fitowa 4:27kusan 1491 K.H.
Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi cikin hamada ka sadu da Musa.” Sai ya sadu da Musa a dutsen Allah, ya sumbace shi.
- Fitowa 4:28kusan 1491 K.H.
Sai Musa ya gaya wa Haruna dukan abin da Ubangiji ya aike yă faɗa, da kuma dukan mu’ujizan da ya umarce shi yă aikata.
- Fitowa 4:29kusan 1491 K.H.
Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa,
- Fitowa 4:30kusan 1491 K.H.
sai Haruna ya gaya musu dukan abin da Ubangiji ya ce wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a gaban mutanen,
- Fitowa 4:31kusan 1491 K.H.
sai suka gaskata. Sa’ad da suka ji cewa Ubangiji ya damu da su, ya kuma ga azabarsu, sai suka durƙusa suka yi sujada.