Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Moses & The Exodus

God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.

415 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Fitowa 6:3kusan 1491 K.H.

    Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba.

  2. Fitowa 6:4kusan 1491 K.H.

    Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci.

  3. Fitowa 6:5kusan 1491 K.H.

    Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.

  4. Fitowa 6:6kusan 1491 K.H.

    “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku.

  5. Fitowa 6:7kusan 1491 K.H.

    Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa.

  6. Fitowa 6:8kusan 1491 K.H.

    Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ”

  7. Fitowa 6:9kusan 1491 K.H.

    Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.

  8. Fitowa 6:10kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  9. Fitowa 6:11kusan 1491 K.H.

    “Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.”

  10. Fitowa 6:12kusan 1491 K.H.

    Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”

  11. Fitowa 6:13kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.

  12. Fitowa 6:14kusan 1491 K.H.

    Waɗannan su ne shugabannin iyalansu. ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne, Hanok da Fallu, Hezron da Karmi. Waɗannan su ne dangin Ruben.

  13. Fitowa 6:15kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana. Waɗannan su ne dangin Simeyon.

  14. Fitowa 6:16kusan 1491 K.H.

    Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.

  15. Fitowa 6:17kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne, Libni da Shimeyi.

  16. Fitowa 6:18kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133.

  17. Fitowa 6:19kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Merari maza, su ne, Mali da Mushi. Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.

  18. Fitowa 6:20kusan 1491 K.H.

    Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137.

  19. Fitowa 6:21kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Izhar maza, su ne, Kora, Nefeg da Zikri.

  20. Fitowa 6:22kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Uzziyel maza, su ne, Mishayel, Elzafan da Sitri.

  21. Fitowa 6:23kusan 1491 K.H.

    Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.

  22. Fitowa 6:24kusan 1491 K.H.

    ’Ya’yan Kora maza, su ne, Assir, Elkana da Abiyasaf. Waɗannan su ne dangin Kora.

  23. Fitowa 6:25kusan 1491 K.H.

    Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi.

  24. Fitowa 6:26kusan 1491 K.H.

    Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.”

  25. Fitowa 6:27kusan 1491 K.H.

    Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.