- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Moses & The Exodus
God raises up Moses to confront Pharaoh; the ten plagues culminate in Israel's dramatic deliverance from four centuries of bondage.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 5:1kusan 1491 K.H.
Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”
- Fitowa 5:2kusan 1491 K.H.
Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”
- Fitowa 5:3kusan 1491 K.H.
Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”
- Fitowa 5:4kusan 1491 K.H.
Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!”
- Fitowa 5:5kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Fir’auna ya ce, “Ga shi mutane sun yi yawa a ƙasar Masar, ku kuma yanzu kuna so ku hana su yin aiki.”
- Fitowa 5:6kusan 1491 K.H.
A wannan rana Fir’auna ya ba da wannan umarni wa shugabannin masu gandu,
- Fitowa 5:7kusan 1491 K.H.
“Kada ku ƙara ba wa mutanen ciyawar tattaka domin su yi tubula, bari su tafi su tattara tattaka da kansu.
- Fitowa 5:8kusan 1491 K.H.
Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’
- Fitowa 5:9kusan 1491 K.H.
Ku sa waɗannan mutane su yi aiki mai tsanani sosai, don kada su sami zarafin kasa kunne ga maganganun ƙarya.”
- Fitowa 5:10kusan 1491 K.H.
Sai shugabannin masu aikin gandu suka fita suka gaya wa mutanen Isra’ila, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku tattaka ba.
- Fitowa 5:11kusan 1491 K.H.
Ku tafi ku nemo wa kanku tattaka duk inda za ku samu, amma ba za a rage aikinku ba ko kaɗan.’ ”
- Fitowa 5:12kusan 1491 K.H.
Saboda haka mutane suka warwatsu ko’ina a Masar domin tattara bunnun da za su yi amfani da su, maimakon tattaka.
- Fitowa 5:13kusan 1491 K.H.
Shugabannin gandu suka dinga matsa musu suna cewa, “Ku cika aikin da aka bukace ku na kowace rana kamar yadda kuke yi sa’ad da kuke da tattaka.”
- Fitowa 5:14kusan 1491 K.H.
Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?”
- Fitowa 5:15kusan 1491 K.H.
Sai manyan Isra’ila masu bi da aikin gandu suka tafi wurin Fir’auna suka yi roƙo suna cewa, “Don me kake yi wa bayinka haka?
- Fitowa 5:16kusan 1491 K.H.
Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.”
- Fitowa 5:17kusan 1491 K.H.
Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’
- Fitowa 5:18kusan 1491 K.H.
Ku ɓace yanzu daga nan, ku koma wurin aikinku. Ba za a ba ku tattaka ba, kuma dole ku fid da tubula kamar yadda kuka saba.”
- Fitowa 5:19kusan 1491 K.H.
Manyan Isra’ilawa da suke bi da aikin gandu suka gane cewa sun shiga uku, sa’ad da aka gaya musu, “Ba za ku rage yawan tubulan da aka bukace ku ku yi na kowace rana ba.”
- Fitowa 5:20kusan 1491 K.H.
Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su,
- Fitowa 5:21kusan 1491 K.H.
sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.”
- Fitowa 5:22kusan 1491 K.H.
Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan?
- Fitowa 5:23kusan 1491 K.H.
Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.”
- Fitowa 6:1kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
- Fitowa 6:2kusan 1491 K.H.
Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji.