Tsallake zuwa abun ciki

Judah

244 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Judas, Juda

Ayoyin da suka ambaci Judah

Tace bisa littafi
  1. Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar.

  2. Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,

  3. Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.”

  4. Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi.

  5. Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki.

  6. A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa.

  7. Amma ga Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da mulki a kansu.

  8. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka aika, suka kira shi zuwa taro, suka kuma naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. Kabila Yahuda kaɗai ta kasance mai biyayya ga gidan Dawuda.

  9. Da Rehobowam ya isa Urushalima, ya tattara dukan gidan Yahuda da kabilar Benyamin, ya sami sun kai mayaƙa dubu da tamanin. Sai aka shirya don su yaƙi gidan Isra’ila, su kuma mayar da masarautar wa Rehobowam ɗan Solomon.

  10. “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon, sarkin Yahuda, ka faɗa wa dukan gidan Yahuda da Benyamin, da kuma dukan sauran mutane,

  11. In waɗannan mutane sun riƙa haurawa don su miƙa hadayu a haikalin Ubangiji a Urushalima. Za su sāke nuna biyayya ga mai girma, Rehobowam, sarkin Yahuda. Za su kashe ni su kuma koma ga Sarki Rehobowam.”

  12. Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi.

  13. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya.

  14. Mahaifinsu ya tambaye su ya ce, “Wace hanya ce ya bi?” Sai ’ya’yansa suka nuna masa hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi.

  15. Ya bi bayan mutumin Allah. Ya same shi yana zama a ƙarƙashin itace oak, sai ya tambaye shi ya ce, “Kai ne mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda?” Ya amsa, “Ni ne.”

  16. Sai tsohon annabin ya tā da murya wa mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ƙazantar da maganar Ubangiji, ba ka kuma kiyaye umarnin Ubangiji Allahnka ba.

  17. Rehobowam ɗan Solomon ya zama sarki a Yahuda. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekaru goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila don yă sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita mutuniyar Ammon ce.

  18. Yahuda ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Ta wurin zunuban da suka yi, sun tā da fushin kishinsa fiye da yadda kakanninsu suka yi.

  19. Game da sauran ayyukan mulkin Rehobowam kuwa, da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  20. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda,

  21. Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam.

  22. A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda,

  23. Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.

  24. Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.

  25. Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta.