Skip to content

Onan

6 ayoyi · 6 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Onan

  1. Ta sāke yin ciki, ta haifi wani ɗa, ta kira shi Onan.

  2. Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka kwana da matar ɗan’uwanka ka cika wajibinka gare ta a matsayin ɗan’uwan miji, don ka samar wa ɗan’uwanka ’ya’ya.”

  3. Amma Onan ya san cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba; saboda haka a duk sa’ad da ya kwana da matar ɗan’uwansa, sai yă zub da maniyyinsa a ƙasa don kada yă samar wa ɗan’uwansa ’ya’ya.

  4. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  5. Er da Onan, ’ya’yan Yahuda ne, amma sun mutu a Kan’ana.

  6. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.