Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shelah

8 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ta kuma haifi wani ɗa har yanzu, aka kuwa ba shi suna Shela. A Kezib ne ta haife shi.

  2. Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar ’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta.

  3. sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.

  4. Yahuda ya gane su, sai ya ce, “Ai, ta fi ni gaskiya, da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Bai kuwa ƙara kwana da ita ba.

  5. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana). ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.

  6. Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu, daga Shela, kabilar Shelayawa daga Ferez, kabilar Ferezawa; daga Zera, kabilar Zerawa;

  7. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.

  8. ’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya,