Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.

  2. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.

  3. Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.

  4. Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.

  5. Yana nan tare da Allah tun farar farawa.

  6. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.

  7. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

  8. Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.

  9. Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.

  10. Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.

  11. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.

  12. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.

  13. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah

  14. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

  15. (Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”)

  16. Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.

  17. Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.

  18. Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.

  19. Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”

  20. Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”

  21. suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”

  22. Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.

  23. Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!

  24. Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’

  25. Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”