Jesus
An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ
Ayoyin da suka ambaci Jesus
Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki.
Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima.
Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.
Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”
Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”
Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?”
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”
Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?”
Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne.
Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.
To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa.
Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane.
Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.
Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.
Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”
Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba?
Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu.
Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?
Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.
Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,
don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”