Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa.

  2. Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

  3. Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”

  4. Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.

  5. Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”

  6. Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

  7. Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”

  8. Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

  9. Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”

  10. Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”

  11. Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.

  12. Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.”

  13. Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan.

  14. Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

  15. Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin.

  16. Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.

  17. Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,

  18. ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ”

  19. Sai suka tuna da maganarsa.

  20. Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.

  21. Amma ba a ba su ikon gane shi ba.

  22. Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu.

  23. Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”

  24. Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.

  25. Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.