Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

  2. Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.

  3. Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga.

  4. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”

  5. Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.

  6. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

  7. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.

  8. A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.

  9. Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.

  10. Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.

  11. Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

  12. An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.

  13. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,

  14. suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

  15. Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,

  16. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

  17. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

  18. Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

  19. Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi,lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

  20. Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”

  21. Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha.

  22. Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”

  23. Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.

  24. Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

  25. Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”