Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Ya kuma ce, “Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.”

  2. Da kuma, “Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai, ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”

  3. Kuma Ishaya ya ce, “Tushen Yesse zai tsiro, wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai; al’ummai za su sa bege a gare shi.”

  4. in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

  5. Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah.

  6. Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata

  7. ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi.

  8. Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa.

  9. Sai dai kamar yadda yake a rubuce, “Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani, waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”

  10. Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.

  11. Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni.

  12. Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.

  13. Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu.

  14. Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.

  15. Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.

  16. Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.

  17. Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.

  18. Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.

  19. Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon. Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.

  20. Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.

  21. Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni.

  22. Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.

  23. Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.

  24. Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.

  25. Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.