Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa.

  2. Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi.

  3. kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”

  4. ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

  5. Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah.

  6. Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni.

  7. Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

  8. Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!

  9. Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.

  10. Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

  11. Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko.

  12. Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.

  13. Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo.

  14. Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu.

  15. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  16. “An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.

  17. Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.

  18. Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam!

  19. Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.”

  20. Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.

  21. Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta.

  22. Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta.

  23. Duk da haka, sai kowa yă kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan.

  24. Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi.

  25. To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji.