Tsallake zuwa abun ciki

Isaac

123 ayoyi · 12 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Isaac

Tace bisa littafi
  1. Bayan Ishaku ya gama sa masa albarka, Yaƙub yana fita daga mahaifinsa ke nan, sai ga ɗan’uwansa Isuwa ya dawo daga farauta.

  2. Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?” Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”

  3. Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”

  4. Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?”

  5. Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni’imar ƙasar za tă nisanci mazauninka. Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za tă nisance ka.

  6. Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”

  7. Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.

  8. Sa’an nan Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan Aram, zuwa wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram. Laban ne ɗan’uwan Rebeka, wadda take mahaifiyar Yaƙub da Isuwa.

  9. Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,”

  10. Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba;

  11. A can bisantaUbangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai.

  12. ya kuma kora dukan dabbobinsa, suka ja gabansa, tare da dukan abubuwan da ya samu a Faddan Aram, don su tafi wurin mahaifinsa Ishaku a ƙasar Kan’ana.

  13. Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”

  14. Bari Allah na Ibrahim da Allah na Nahor, Allah na iyayensu, yă zama alƙali tsakaninmu.” Saboda haka Yaƙub ya yi rantsuwa da sunan Tsoron mahaifinsa Ishaku.

  15. Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’

  16. Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.”

  17. Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna.

  18. Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin,

  19. sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.

  20. Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.

  21. Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,

  22. Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”

  23. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.

  24. Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.”

  25. Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub.