Tsallake zuwa abun ciki

Isaac

123 ayoyi · 12 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Isaac

Tace bisa littafi
  1. Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.

  2. Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan.

  3. “Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar.

  4. Ubangiji ya ce, “Wannan zai sa su ba da gaskiya cewa Ubangiji, Allah na kakanninsu, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah da Yaƙub, ya bayyana gare ka.”

  5. Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba.

  6. Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ”

  7. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”

  8. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’

  9. zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.

  10. ‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,

  11. Duba na riga na ba ku wannan ƙasa. Ku shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub, da kuma ga zuriyarsu bayansu.”

  12. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba,

  13. Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.

  14. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Kada ka kula da taurinkan, mugunta da kuma zunubin wannan mutane.

  15. don yă mai da ku jama’arsa yau, shi kuwa yă zama Allahnku kamar yadda ya yi muku alkawari, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.

  16. don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.

  17. Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”

  18. Amma na ɗauki mahaifinku Ibrahim, daga ƙasar da take can a hayin Kogin Yuferites, na kawo shi ƙasar Kan’ana, na kuma ba shi ’ya’ya masu yawa. Na ba shi Ishaku,

  19. ga Ishaku kuwa na ba shi Yaƙub da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar kan tudu ta Seyir, amma Yaƙub da ’ya’yansa maza suka gangara zuwa Masar.

  20. A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka.

  21. Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba.

  22. ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.

  23. Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila.

  24. alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.

  25. Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.