Kiriath-arba
An kuma san shi da: Arbah, Kirjath-arba
31.5300, 35.0900 Duba a Google Maps
Ayoyin da suka ambaci Kiriath-arba
Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.
Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna.
(Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.
Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.
Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda.
Suka ci gaba suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron (wadda dā ake kira Kiriyat Arba) suka kuma ci Sheshai, Ahiman da Talmai da yaƙi.
Game da ƙauyukan da filayensu, waɗansu mutanen Yahuda suka zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta.