Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. ’Yan’uwa, salama tare da ƙauna da kuma bangaskiya daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.

  2. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare ku.

  3. Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.

  4. Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.

  5. cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.

  6. ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne.

  7. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

  8. Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

  9. kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.

  10. gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

  11. don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya

  12. Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.

  13. Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.

  14. Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,

  15. a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.

  16. ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.

  17. Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.

  18. Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya.

  19. Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

  20. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  21. Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  22. An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

  23. Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  24. Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.

  25. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,