God
Ayoyin da suka ambaci God
Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’
In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’
“Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan.
A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji, “kashi biyu bisa uku za a buge su su hallaka; duk da haka za a bar kashi ɗaya bisa uku a cikinta.
Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”
Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku.
Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba.
Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi.
A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu.
Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki.
Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske.
Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.
Ga bala’in da Ubangiji zai bugi dukan al’umman da suka yi yaƙi da Urushalima. Fatar jikinsu za tă ruɓe tun suna tsaye a ƙafafunsu, idanunsu za su ruɓe a cikin kwarminsu, harsunansu kuma zai ruɓe a cikin bakunansu.
A ranan nan Ubangiji zai sa maza su cika da tsoro ƙwarai. Kowane mutum zai kama hannun ɗan’uwansa, za su kai wa juna hari.
Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul.
In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba.
In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.
A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade.
Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.
Annabci, wannan ita ce maganar Ubangiji ga Isra’ila ta wurin Malaki.
“Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub,
amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”
Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji.
Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’
“Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’