God
Ayoyin da suka ambaci God
“Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.
Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi, zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi. ’Ya’yansu za su gani su yi murna; zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.
Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā.
Ko da yake na warwatsa su cikin mutane, duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni. Su da ’ya’yansu za su rayu, za su kuwa komo.
Zan komo da su daga Masar in kuma tattara su daga Assuriya. Zan kawo su Gileyad da Lebanon, har wuri yă kāsa musu.
Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,” in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka.
Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba.
Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”
An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.
Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi.
Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu.
Annabci, maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji, wanda ya shimfiɗa sammai, wanda ya kafa harsashin duniya, wanda kuma ya yi ruhun mutum a cikinsa ya ce,
“Zan sa Urushalima ta zama kwaf mai sa mutanen da suke a dukan kewayenta, jiri. Yaƙi zai kewaye Urushalima har yă shafi Yahuda ma.
A ranan nan, sa’ad da duk al’umman duniya za su tayar mata, zan sa Urushalima ta zama dutsen da ba a iya matsarwa ga dukan al’ummai. Duk waɗanda suka yi ƙoƙari su matsar da shi za su ji ciwo.
A ranan nan zan sa kowane doki yă tsorata, mai hawan dokin kuma yă haukace,” in ji Ubangiji. “Zan sa idanuna in tsare gidan Yahuda, amma zan makantar da dukan dawakan al’ummai.
Sa’an nan shugabannin Yahuda za su ce a cikin zukatansu, ‘Mutanen Urushalima suna da ƙarfi domin Ubangiji Maɗaukaki shi ne Allahnsu.’
“A ranan nan zan sa shugabannin Yahuda su zama kamar tukunyar wuta a tarin itacen wuta; kamar harshen wuta a dammunan hatsi. Za su ƙone dukan mutanen da suke kewaye da su hagu da dama, amma babu abin da zai taɓa mutanen Urushalima.
“Ubangiji zai ceci wuraren zaman Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dawuda da mazaunan Urushalima su fi na Yahuda daraja.
A ranan nan Ubangiji zai kiyaye waɗanda suke zama a Urushalima, domin marasa ƙarfi a cikinsu su zama kamar Dawuda, gidan Dawuda kuma zai zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji da yake tafiya a gabansu.
A ranan nan zan fito don in hallaka dukan al’umman da suka yaƙi Urushalima.
“Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari.
“A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar.
In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi.