Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Za a ba Heldai, Tobiya, Yedahiya da kuma Hen ɗan Zefaniya kamar abin tunawa a cikin haikalin Ubangiji.

  2. Waɗanda suke nesa za su zo su taimaka gina haikalin Ubangiji, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Wannan zai faru in kuka yi biyayya sosai ga Ubangiji Allahnku.”

  3. A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb.

  4. Mutanen Betel sun aika Sharezer da Regem-Melek, tare da mutanensu su nemi tagomashin Ubangiji

  5. ta wurin tambayar firistocin da kuma annabawan gidan Ubangiji Maɗaukaki, “Ko ya kamata in yi makoki da azumi a wata na biyar, yadda na yi a shekaru masu yawa?”

  6. Sai maganar Ubangiji Maɗaukaki ta zo mini ta ce,

  7. “Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi?

  8. Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ”

  9. Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa,

  10. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.

  11. Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.

  12. “ ‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  13. ‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’ ”

  14. Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa gare ni.

  15. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.”

  16. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.”

  17. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa.

  18. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.

  19. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Zan ceci mutanena daga ƙasashen gabas da yamma.

  20. Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.”

  21. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku da yanzu kuke jin maganan nan da annabawa suka faɗi, waɗanda suke a nan lokacin da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji Maɗaukaki, bari hannuwanku su zama da ƙarfi don a gama gina haikalin.

  22. Kafin wannan lokaci babu albashi domin mutum ko dabba. Ba wanda yake iya sakewa yă yi hidimominsa saboda maƙiya, domin na sa kowa yă zama maƙiyi maƙwabcinsa.

  23. Amma yanzu ba zan yi da waɗanda raguwar mutane yadda na yi da na dā ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  24. “Iri zai yi girma da kyau, kuringa za tă ba da ’ya’yanta, ƙasa za tă ba da hatsi, sama kuma za tă ba da raɓa. Zan ba da duk waɗannan abubuwa su zama gādo ga raguwar mutanen nan.

  25. Kamar yadda kuka zama abin la’ana a ƙasashe, ya Yahuda da Isra’ila, haka zan cece ku, za ku kuma zama albarka. Kada ku ji tsoro, sai dai ku bar hannuwanku su zama da ƙarfi.”