God
Ayoyin da suka ambaci God
amma ba su gane cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba. Zunubansu sun kewaye su; kullum suna a gabana.
Dukansu suna da zafi kamar matoya; suna kashe masu mulkinsu. Dukan sarakunansu sukan fāɗi, kuma babu waninsu da yake kira gare ni.
Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa, amma duk da haka bai dawo ga Ubangiji Allahnsa ko yă neme shi ba.
Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu; zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama. Sa’ad da na ji suna tafiya tare, zan kama su.
Kaitonsu, domin sun kauce daga gare ni! Hallaka za tă aukar musu, domin sun tayar mini! Na ƙudura in cece su amma suna faɗar ƙarya a kaina.
Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu amma suna ihu a kan gadajensu. Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi amma su juya mini baya.
Na horar da su na kuma ƙarfafa su, amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.
Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka; suna kama da tanƙwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi saboda banzan maganganunsu. Saboda wannan za a wulaƙanta su a ƙasar Masar.
“Ka sa kakaki a leɓunanka! Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji domin mutane sun tā da alkawarina suka kuma tayar wa dokata.
Isra’ila ta yi mini kuka, ‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’
Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba; sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba. Da azurfa da zinariya sun ƙera gumaka wa kansu wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.
Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka?
Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya.
Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai, yanzu zan tattara su wuri ɗaya. Za su fara lalacewa a ƙarƙashi danniyar babban sarki.
Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata, amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.
Suna miƙa hadayun da aka ba ni su kuma ci nama, amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta zunubansu. Za su koma Masar.
Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa ya kuma gina fadodi; Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa. Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu da zai cinye kagaransu.”
Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila; kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai. Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku; kuna son hakkokin karuwa a kowace masussuka.
Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba; Efraim zai koma Masar yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.
Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba, ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba. Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki; duk wanda ya ci su zai ƙazantu. Wannan abincin zai zama na kansu ne; ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba.
Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku, a ranakun bikin Ubangiji?
Annabi, tare da Allahna, su ne masu tsaro a bisa Efraim, duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi, da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.
Sun nutse da zurfi cikin lalaci, kamar a kwanakin Gibeya. Allah zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta su saboda zunubansu.
“Sa’ad da na sami Isra’ila, ya zama kamar samun inabi a hamada; sa’ad da na ga kakanninku, ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure. Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor, suka keɓe kansu wa gumaka bankunya sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.
Ko da sun yi renon ’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya!