Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba; za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba, gama sun rabu da Ubangiji don su ba da kansu

  2. Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace suka kuwa sami amsa daga sanda. Halin karuwanci yakan ɓad da su; sun yi rashin aminci ga Allahnsu.

  3. “Ba zan hukunta ’ya’yanku mata sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba, balle surukanku mata, sa’ad da suka yi zina, gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada, mutane marasa ganewa za su lalace!

  4. “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’

  5. Isra’ilawa masu taurinkai ne, kamar karsana mai taurinkai. Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?

  6. ’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla. Zan hore su duka.

  7. Na san Efraim ƙaf; Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba. Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci; Isra’ila ta lalace.

  8. “Ayyukansu ba su ba su dama su koma ga Allahnsu ba. Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu; ba su yarda da Ubangiji ba.

  9. Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu don su nemi Ubangiji, ba za su same shi ba; ya janye kansa daga gare su.

  10. Su marasa aminci ne ga Ubangiji; suna haihuwar shegu. Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu za su cinye su da gonakinsu.

  11. Efraim za tă zama kango a ranar hukunci. A cikin kabilan Isra’ila na yi shelar abin da yake tabbatacce.

  12. Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne. Zan zubo musu da fushina a kansu kamar rigyawar ruwa.

  13. Na zama kamar asu ga Efraim, kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.

  14. Gama zan zama kamar zaki ga Efraim, kamar babban zaki ga Yahuda. Zan yage su kucu-kucu in tafi; zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.

  15. Sa’an nan zan koma wurina sai sun yarda da laifinsu. Za su kuma nemi fuskata; cikin azabansu za su nace da nemana.”

  16. “Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu.

  17. Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa.

  18. Bari mu yarda da Ubangiji; bari mu nace gaba don mu yarda da shi. Muddin rana tana fitowa, zai bayyana; zai zo mana kamar ruwan bazara, kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”

  19. “Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.

  20. Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana, na kashe ku da kalmomin bakina; hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.

  21. Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.

  22. Kamar Adamu, sun tā da alkawari, sun yi mini rashin aminci a can.

  23. Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu.

  24. “Ku kuma, ya mutanen Yahuda, na shirya muku ranar girbi. “A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,

  25. a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;