Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa.

  2. Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.

  3. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku yadda ya alkawarta, ku kiyaye wannan biki.

  4. Sai ku faɗa musu, ‘Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ ” Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada.

  5. Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

  6. Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi.

  7. A cikin daren, Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Ku tafi, ku bauta wa Ubangiji yadda kuka ce.

  8. Ubangiji kuwa ya sa Isra’ilawa suka yi farin jini a wurin Masarawa, Masarawa kuma suka saki hannu wa mutanen, suka ba su duk abin da suka roƙa; ta haka Isra’ilawa suka washe Masarawa.

  9. A ranar da shekara 430 ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan ɓangare-ɓangare na mutanen Ubangiji suka bar Masar.

  10. Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa.

  11. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Waɗannan ne ƙa’idodin Bikin Ƙetarewa. “Ba baƙon da zai ci shi.

  12. “Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa.

  13. Dukan Isra’ilawa suka yi na’am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

  14. A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar.

  15. Ubangiji ya ce wa Musa,

  16. “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

  17. Sai Musa ya ce wa mutane, “Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga ƙasar bauta, gama Ubangiji ya fito da ku da hannu mai iko. Kada ku ci wani abin da yake da yisti.

  18. Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata.

  19. Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, a kan rana ta bakwai kuma za ku yi biki ga Ubangiji.

  20. A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’

  21. Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko.

  22. Dole ku kiyaye wannan farilla kowace shekara a lokacinta.

  23. “Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku,

  24. sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne.

  25. “A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta.